Kimanin Naira Biliyan 100 Za’a  Kashe A Shirin Bunkasa Kiwon Dabbobi

Majalisar Tattalin Arzikin kasar Najeriya  ta bayyana cewa shirin bunkasa kiwo na zamani ba zai karkata ne kawai ga bunkasa kiwon shanu ba, zai hada da magance abubuwan da suke kawo cikas ga kiwon sauran dabbobi.

A karkashin shirin, za a kashe naira biliyan 100, inda Gwamnatin Tarayya zata ba da kashi 80 na kudin yayin da jihohi za su bada gudumuwar filaye, tsare-tsaren aiwatar da ayyukan, jami’ai da kuma kashi 20 na kudin kafa shirin.

Gwamna Jahar Ebonyi Dabid Umahi, ya bayyana hakan ne  a lokacin da yake  jawabi ga manema labarai na fadar shugaban kasa, jim kadan bayan kammala taron majalisar tattalin arzikin kasa bisa jagorancin mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo.

Inda ya bayyana  cewar makasudin shirin shi ne ya kawo karshen rikicin da ake yi a tsakanin makiyaya da manoma.

Shugaban Majalisar Tattalin Arzikin Kasa ya tunatar da mu cewa babban burin majalisar shi ne lalubo bakin zaren rikicin manoma da makiyaya.

Kwamitin majalisar ya gabatar da tsarin da za a bi a shawo kan lamarin da za a yi aiki da shi daga 2019 zuwa 2028, ba kiwon shanu kawai za a bunkasa ba, har da sauran dabbobi na gida da ake kiwo.

Umahi ya ce tsarin ya kunshi muhimman ayyuka guda shida da suka hada da warware sabani, yin adalci ga kowa da tabbatar da zaman lafiya, ba da agaji ga al’umma, samar da kwararan ma’aikata da sauran batutuwa da suka kunshi bunkasa tattalin arzikin na Najeriya.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More