Kiris ya rage masu Coronavirus su kai 2000 a Najeriya

Hukumar da ke dakile yaduwar cutuka ta Najeriya wato NCDC ta tabbatar da cewa, mutune 204 me suka sake kamuwa da Coronavirus a Najeriya, wanda hakan ya sa addadin masa cutar suka kai 1,932 a kasar ta Najeriya.

Sabbin wayanda suka kamun sune:
80-Kano
45-Lagos
12-Gombe
9-Bauchi
9-Sokoto
7-Borno
7-Edo
6-Rivers
6-Ogun
4-FCT
4-Akwa Ibom
4-Bayelsa
3-Kaduna
2-Oyo
2-Delta
2-Nasarawa
1-Ondo
1-Kebbi

Daga karfe 11:50 na daren ranar Alhamis 30 ga watan Aprilu 2020, hukumar ta NCDC ta tabbatar da jumullar mutuwar mutane 58, yayin mutane 319 suka warke daga cutar a shafin ta na twitter.

Har yanzu jahar Legas, inda Coronavirus ta fara bulla a Najeriya ce ke kan gaba a yawan mutanen da suka kamu da cutar inda a yanzu take da mutune 976.

A yanzu dai Jahar Kogi da Cross river ne kawai a Najeriya annobar ba ta kai gare su ba.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More