Kiris ya raje jirgin Ethiopia kifar da obasanjo a Legos

Tsohon shugaban kasar Najeriya  Cif Olesegun Obasanjo tare da wasu ‘yan Najeriya sun tsallake rijiya da baya a wani hadarin jirgin sama da ya tashi afkuwa yayin sauka a filin jirgin saman Murtala Muhammad dake jahar Legos.

A cikin jirgin na kasar Ethiopia, akwai manya sannanun ‘yan kasa da su ka hada da babban Darakta na kungiyar kasuwanci, masana’antu, noma da ma’adinai, Ambasada Ayoola Olukanni, sai kuma Daraktan hukumar NAFDAC, Farfesa Samson Tunde Adedayo hadi da wasu fitattun manyan ‘yan Najeriya.

Jirgin dai, ya taso ne daga kasar Ethiopia a babban filin jirgin kasar da misalin karfe 9 na safe, daidai da misalin karfe 7 na safiya a  Najeriya.

Jirgin dai, wanda zai yi tafiyar awa biyar kafin sauka, lafiya yake tafiya ba tare da wata matslaa ba har lokacin da ya zo sauka a filin jirgin saman Murtala Muhammad da ke Legas. Jirgin dai ya samu matsalar sauka ne saboda matsalar ruwa da iska a lokacin, sai bai dira kan layin titin da ya kamata ya sauka ba, inda  matukin jirgin, ya samu nasarar daukar matakin gaggawa na juya akalar jirgin  ya koma sararin samaniya. Jirgin ya sake sauka bayan shawagin minti kusan 20 a sararin sama tsakanin jahar ta Legas da Ogun.

 

 

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More