Ko  menene dalilin da yasa baza’a kai karar Afrika ta Kuda majaisar dinkin duniya ba?

Ministan harkokin wajen Najeriya, Geoffrey Onyeama, ya ce gwamnatin Najeriya ba za ta kai karan kasar Afirka ta kudu majalisar dinkin duniya ba kan cin zarafin yan Najeriya a taron gangamin da zai gudana a wannan watan a birnin New York, dake kasar Amurka.
 
Ministan ya kara da cewa ana tattaunawar diflomasiyya kan ganin yadda za’a biya yan Najeriya da abin ya sha wasu kudade.
 
Da aka tambayesa shin za suyi magana kan harin kin jinin bakin fatan da aka kaiwa yan Najeriya a kasar Afrika ta kudu.
 
Sai dai cewa yayi Ba’a kai ga wannan wurin ba, kuma baya tunanin ana bukatar hakan domin abune da zamu iya tattaunawa tsakaninmu.
 
A ranar Litinin ne shugaba Muhammadu Buhari ya amince da hakurin shugaban kasar Afirka ta kudu, Cyril Ramaphosa, kan hare-haren da aka kaiwa yan Najeriya a kasarsa.
 
Shugaba Buhari, wanda ya siffanta wannan hare-hare a matsayin abin takaici ya ce duk da hakan, za’a cigaba da karfafa alaka tsakanin kasashen guda biyu.
 
Buhari ya tunawa wakilan shugaban kasan irin namijin gudunmuwar da Najeriya ta baiwa kasar Afirka ta kudu saboda yawancin matasan kasar sun jahilci tarihi.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More