Ko menene dalilin da yasa Sarki Sanusi bai gaisa da sabbin sarakunan wajen taron Wudil ba ?

An yi kallon-kallo tsakanin sarakunan jahar Kano a wajen taron yaye hafsohin ‘yan sanda da aka gudanar a garin Wudil dake jahar.
Sarakunan jahar Kano guda biyar sun fara haduwa da juna a wajen ne, tun da aka kafa sabbin masarautu hudun na jahar.
Sarki Muhammadu Sanusi II ya isa wajen taron ne bayan sarakunan Bichi, Rano,Gaya da kuma Karaye, wadanda hakimai ne a masarautar Kano kafin gwamnatin jahar ta nada su sarakunan yankin a sabbin masarautun da aka kirkiro a ‘yan watannin baya da suka wuce.
Sai dai sabbin sarakunan ba su gaisa da Sarki Sanusi ko yin magana da shi ba balle kuma nuna sanayya har aka kallamala taron.

Hakan ta sa aka yi mamaki, duba da dadaddiyar sanayyar da ke tsakaninsu da kasancewar dukkansu ‘yan majalisar masarautun jahar ne kuma manyan baki a wajen taron.
Wakilin BBC da ya halarci wajen taron, yayin da ya gane wa da idon sa, ya ce yayin da Sarki Sanusi ya iske sauran sarakunan zaune a kusa da juna, tawagarsa ta iske wani basarake daga babban birnin tarayyar kasar Abuja, zaune a kujerar Sarki Sunusi a wurin.
Sakamakon haka ne aka ware wa sarkin wani wurin zama, abin da wasu ke gani a matsayin kaskantar ga shugaban majalisar sarakunan jahar.
Bayan zuwan shugaban kasa Muhammadu Buhari taron ne aka sauya wa Sarki Sanusi wurin zama inda ya koma kusa da shugaba Buhari a teburin da aka ware wa manyan bakin alfarma.

A karshen taron dai shugaban kasar ya gaisa da Sarkin Kano Sunusi, amma sauran sarakunan ba su samu damar yin hakan ba, kasancewar Sarki Sunusi ne kadai a cikin su yake sahun farko na manyan baki da ke kusa da shugaban kasar.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More