Ko tsirara zaki saka hoton mu sai mu auru, martanin Sadiya Kabala ga jakadiyyar tonan asiri Menene ra’ayin ku game da hakan?

Jarumar fina-finan hausa wacce aka sani da Sadiya Kabala, ta mayarwa da jakadiyar tonon asiri

martani kan wani rubutu da jakadiyar ta wallafa a kanta, hakka bashi karo na  farkon  da ake kace-nace tsakanin jaruman fina-finan hausa da jakadiyar tonon asiri ba, musamman mata.

Jakadiyar ta wallafa hoton Sadiya cikin shiga ta kamala da hijabi a kasa ta rubuta:

Wallahi da zaki ma kanki fada ki koma sa hijab da kinfi kyau sosai baki ga yadda hijab nan yayi miki kyau ba, saboda rashin mutunci har zuwa wajen motsa jiki kike yi, hmmm Allah ya shiryeki Sadiya Kabala.”

Martanin Sadiya Kabala ga jakadiyar tonan asiri:

“Dama idan ruwa ya karewa dan kada sai ya koma tunkuri, ashe kina nan jiya ko na gama cigiyarki na jiki shiru kwana biyu, dama na kosa na samu masoya miliyan daya a taimaka a nemo mai zafi a dora domin wannan ba zai saka mutane su biyo ni ba. Dan Allah ki nemo mai zafi ki saka. “Iyayen leke-leke ke kofa a tsirara zaki samu wallahi sai mun auru dan ba kanmu farau ba kuma ba kanmu karshe ba.”

Jakadiyar tonan asiri  tayi suna sosai a shafin Instagram wajen tona asiri tare da bankado duk wani abu na Allah wadai da jaruman fim suke yi tana yadawa duniya ta gani.Sai dai har  zuwa yanzu an kasa gano ainihin mai amfani da shafin, shin macece ko namiji?

Abin na jakadiyar ba wai ya tsaya akan jaruman fim bane kawai hatta yayan manya mata, yan bariki da dai duk wani mai yin katobara a shafukan yanar gizo idan har hoto ko bidiyon shi ya ci karo da jakadiya to zai ta afa shi duniya ta gani.

A kwanakin baya jakadiyar ta zarge Sadiya Kabala ta da kalmar madigo, saboda ta dauki hoto da jaruma Maryama Yahaya, inda aka nuno su sun naniki juna. Duk da dai wannan karon bata jefeta da wata mummunar kalma kamar waccan ba, saboda ta sanya hijabi kawai dai tayi mata gugar zana ne, amma dai hakan bai hana Sadiya Kabala maida mata da martani ba.

 

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More