Kofa a bude take ga duk mai bukatar neman kujerar da nake kai a 2023 – Sanata Danjuma Goje

Tsohon Gwamnan jahar Gombe kuma Sanata mai wakiltar jahar Gombe ta tsakiya wato Muhammad Danjuma Goje ya sanar da murabus dinsa a siyasar tsaya wa takara.

Sanatan ya bayyana hakan ne a lokacin taron mambobin jam’iyyar APC da kuma magoya bayansa a filin wasa na Pantami a ranar Lahadi 8 ga watan Disamba 2019.

Sai dai  bayyana  cewa, hakan ba yana nufin ya bar siyasa kwata-kwata bane, ya yi hakan ne don ba wa sauran yan siyasar jahar masu tasowa damar nuna bajintarsu.

Da izinin Ubangiji idan ina raye zan fito dan yakin neman zabe  a 2023, akwai yan siyasar da ke ganin kamar na dashashe musu tauraruwarsu dan haka lokaci ya yi da zan bar wa na baya wayanda  na tsare a siyasar takara. Daga yanzu kofa  a bude take ga duk mai bukatar neman kujerar sanatan da nake kai a yanzu idan Allah ya kaimu shekarar 2023. Inji Goje

A karshe sanata Goje yace zai cigaba da goyon baya tare da yin biyayya ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari, shugaban majalisar dattijai Ahmed Lawal, shugaban jam’iyyar APC ta kasa Adams Oshiomhole kuma yana nan kan bakan san a goyon bayan Gwamna jahar sa wato Muhammad Inuwa Yahaya. Inda ya mika godiyarsa garesu da suka bashi damar hidimta musu a mataki daban-daban na karamar hukumar, jaha da kuma tarayya.

Sannan nan take  yayi  kyautar naira miliyan 19 ga shuwagabannin jam’iyyar  APC tun daga matakin gunduma har zuwa jahar tare da motoci, a daidaita sahu da babura kyauta.

 

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More