Koh Abba Yusuf zai tabbata dan takara a Kano?

Jam’iyyar PDP ta tabbatar da cewa har yanzu Abba Kabir Yusuf ne ta sani a matsayin ‘Dan takarar ta na Gwamna a Jihar Kano a zaben 2019.

Abba K. Yusuf dai shi ne Surukin tsohon Gwamna Rabiu Musa Kwankwaso. Wani babban Jami’i na Jam’iyyar PDP mai adawa a Hedikwata ya bayyanawa wata Majiyar mu cewa Jam’iyyar ba ta canza sunan Surukin Kwankwaso da Malam Salihu Takai ba kamar yadda rade-radi ya bi ko ina a tsakiyar makon nan

Dan takarar da ake cewa an ba tuta daga baya watau Salihu Sagir Takai tare da tsohon Shugaban Jam’iyya na Jahar  Sanata Mas’ud El-Jibril Doguwa.

Ba mu dai iya tabbatar da gaskiyar wannan dakatarwa da aka ce an yi wa manyan na PDP ba a dalilin yunkurin sake gudanar da zaben fitar da gwani da su kayi bayan an rufe kofar tsaida ‘Dan takara a Kasar yayin da ake ta zanga-zanga a Jihar.

A baya dai an yi zabe wanda Abba Yusuf yayi nasara, sai dai ‘Yan takarar Gwamna a Jahar Kano a karkashin Jam’iyyar ta PDP sun yi watsi da sakamakon zaben wanda aka yi a cikin gidan Surukin tsohon Gwamnan Jihar Kwankwaso.

.

You might also like More from author

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Comment moderation is enabled. Your comment may take some time to appear.