Koh menene dalilin murabus din Sheikh Ibrahim Khalil ?

Daga dukkan alamu ficewar fitaccen malamin addinin Islama kuma shugaban majalisar malamai ta jahar Kano, Sheikh Ibrahim Khalil, daga gwamnatin gwamnan jahar Kano  Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ta hanyar ajiye mukaminsa na mai bada shawara kan ayyuka na musamman, ta kara nuna yadda gwamnatin ke cigaba da zaizayewa duba da babban zaben na kasa ta Najeriya na 2019 na gabatowa.

Hakan ya fito fili ne sakamakon yadda kwanaki kalilan kenan da wani fitaccen malamin addinin Musuluncin kuma kwamandan Hisba na jahar  Kano, wato Malam Ibrahim Daurawa, ya fito karara a hudubarsa ta Juma’a ya soki lamarin yadda a ka nuna bidiyon gwamnan a na zargin ya na amsar cin hanci daga ’yan kwangila.

A lokacin da wakilinmu ya tuntubi malamin don jin ta bakinsa kan dalilinsa na ajiye mukamin, Sheikh Khalil ya bayyana ma sa cewa, a yanzu ba ya son cewa komai game da lamarin, amma dai ya tabbatar ma sa da cewa gaskiya ne batun ajiye mukamin.

Duk da dai malamin bai bayyana  cewa ya fita  daga jam’iyyar APC mai mulkin a jahar ba,

Sai dai kuma mutanen  na raderadin cewar ya shirin hada kayan sa ne dan yakoma PRP, a yanzu haka a na ganin  PRP a matsayin jam’iyyar a take cigaba da samun karbuwa a fadin jahar, saboda yadda zakakuran ’yan siyasa ke faman tsunduma  cikin ta daga jam’iyyar APC  mai mulki  da kuma babbar jam’iyyar adawa  ta PDP.

You might also like More from author

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Comment moderation is enabled. Your comment may take some time to appear.