Kotu ta ba dan takarar APC damar shiga zaben gwamna a Taraba

Kotun ta ba dan takarar jam’iyyar APC damar shiga zaben gwamna a jihar Taraba da za a gudanar ranar Asabar.

Kotun daukaka kara a Abuja ta dakatar da hukuncin farko ne da wata kotun tarayya a Jalingo ta zartar wacce ta haramtawa dan takarar APC Sani Danladi shiga zabe.

An wanke dan takarar ne daga karar da wasu mutanen Taraba hudu suka shigar gaban kotun tarayya a Jalingo suna zarginsa da yin karya wajen bayyana shekarunsa na haihuwa daga takardun haihuwa da na karatu da ya gabatar wa hukumar zabe.

Yakubu Maikasuwa, Lauyan da ke kare dan takarar gwamnan na jam’iyyar APC a Taraba, wanda ya tabbatar wa da BBC da nasarar da suka samu, ya ce hakan na nufin kotun daukaka kara ta yi watsi da hukuncin farko na kotun tarayya kuma yanzu ta ba su ‘yancin shiga zabe.

An kalubalanci dan takarar na APC ne a Kotu bayan da takardun haihuwarsa suka nuna an haife shi a shekarar 1968, yayin da kuma takardunsa na sakandare suka nuna cewa an haife shi a 1977.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More