Kotu ta bada belin Shehu Sani a kan naira miliyan 10

Wata babbar kotu a Abuja ta bayar da belin tsohon sanata Shehu Sani a kan naira miliyan 10.

Jaridar Punch ta ce mai shari’a Inyang Ekwo, ya ba da belin ne bayan EFCC ta gurfanar da Shehu Sani a karon farko tun bayan tsare shi da hukumar ta yi a narar 31 ga watan Disamban 2019.

EFCC na zargin Shehu Sani da laifin karbar rashawar dala 25,000 da sunan zai ba wa manyan jami’an gwamnati.

Alkalin ya yi watsi da bukatar EFCC na ci gada da tsare Shehu Sani wanda lauyansa ya mika bukatar ba da belinsa.

Mai shari’a Inyanga Ekwo ya shardanta wa Shehu Sani kawo wani dan kasa na gari da ya mallaki kadarar naira miliyan 10 a matsayin wanda zai tsaya masa.

Ya kuma bukaci wanda ake karar ya mika kotun takardar fasfonsa sannan ta umurce shi da kar ya fita daga Najeriya ba tare da izinin kotun ba.

BBC ta rawaito cewa zarge-zargen da EFCC ke wa Shehu Sani sun hada da karbar dala 10,000 da sunan mukaddashin shugabanta Ibrahim Magu.

Tana kuma zargin sa da karbar wani dala 15,000 cewa zai ba wa babban alkalin Najeriya toshiyar baki a kan sharia’rsa da ke gaban kuliya.

Sai dai Shehu Sani ya musanta zarge-zargen da ake masa.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More