Kotu Ta Bada Umarnin A Kamo Hadiza Gabon Cikin Awanni 24

Wata kotun karbar korefi-korafe da ke zama a birnin kano, karkashin jagorancin alkali muntari gambo dandago, ta umurci kwamishinan ‘yan sandan jihar kano da ya kamo, jarumar fina- finan hausa, Hadiza Gabon.

Sannan kuma kotun ta umurci kwamishinan ‘yan sandan da ya binciki zargin da mai karar, jarumi Mustapha Naburaska ya shigar a kan zargin cin zarafinsa da Gabon din ta yi masa.
Alkalin ya yanke hukunci ne sakamakon kauracewa zaman kotu da Hadiza Gabon ta yi a yau alhamis.
Kwanakin baya da suka wuce Naburaska ya shigar da karar Gabon kan zargin cin zarafi.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More