Kotu Ta Bada Umarnin Kama Matar Ganduje

Wata kotu da ke babban birnin tarayyar  Abuja ta umarci hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa EFCC da ta kama matar gwamnan Kano  wato Hafsat Ganduje kan zargin karbar na  goro da mai gidanta ya yi a hannun  wasu yan kwangila da ba’a san su waye ba.

An zargi matar gwamnan da hannu dumu dumu a cikin badakalar zargin rashawa da ta kai dala miliyan biyar.

Kotun karkashin mai shari’a Yusuf Halilu ta umarci jam iyyar APC da ta sauya sunan gwamnan a matsayin dan takarar ta na zaben 2019 kan zargin da ake masa.

Wani lauya da ya zauna sauraron shari’ar ya roki kotun da ta bada umarnin karbe dukkan wani kati da zai bawa gwamnan da matarsa damar tsallake kasar cikin gaggawa tare da karbe dukkan kadarorin gwamnan kano Ganduje tare da uwargidanna sa  Hajiya Hafsat Abdullahi Ganduje.

Zargin karbar na goro dai na nuni da samun tangarda cikin takarar gwamnan ganin yadda kungiyoyi da dama ke shiga cikin lamarin tare da bibiyar bahasin maganar.

 

 

 

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More