Kotu ta bayar da belin Babachir

Wata kotun Abuja ta bayar da belin tsohon sakataren gwamnatin tarayya Babachir David Lawal a ranar Laraba.

An ba da shi beli bayan ya shafe kusan sa’o’i 24 a hanun hukumar EFCC da ke yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya.

Tsohon Sakataren Gwamnatin Kasar Babachir David Lawal ya musanta zarge-zarge goma da hukumar EFCC ta gabatar a gaban kotu a kansa, cikin zargin da ake yi masa ya hada da batun almundahana da kuma mallakar wasu kadarori  bisa rashin ka’ida.

Amma kotun a ranar Laraba ta bayar da belinsa da kuma wasu mutane biyu akan naira miliyan 50 da kuma wanda zai tsaya wa kowane a cikinsu.

Kotun ta ce wanda zai tsaya ma kowane a cikinsu sai an tabbatar yana da gida a birnin tarayya Abuja da kuma shaidar biyan haraji na shekaru uku da suka gabata kuma ya kasance mazaunin Abuja.

Kotun ta bayar da umarnin cewa dole ne tsohon sakataren gwamnatin na tarayyar da sauran mutanen biyu su bayar da fasfonsu na tafiye tafiye domin cike sharuddan belin.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More