Kotu ta bukaci a gabatar da sojojin da suka saki Wadume

Wata babbar kotun dake babban birnin tarayyar Abuja ta umarci rundunar sojin kasar ta mika sojojin da ake zargin suna da hannu wajen kubutar da Hamisu Bala, wanda ake wa lakabi da Wadume, bayan ‘yan sanda sun kama shi.

A watan Agustan da ya wuce ‘yan sanda suka kama shi a jahar Taraba, inda suke zarginsa da hannu wajen satar mutane domin karbar kudin fansa.

Yan sanda sun gufarnar da wadume da wasu 18 da aka zargin a yau Litinin 16 ga watan Maris 2020.

Sai dai a wancan lokacin rundunar ‘yan sandan ta zargi wasu sojojin kasar da hallaka jami’anta uku tare da raunata wasu bayan da sojojin suka bude wuta kan tawagar ‘yan sandan da ta kamo Wadume.
Mai shari’a Binta Nyako ta umurci manyan jami’an sojojin, wato da babban hafsan hafsoshin sojin Najeriya, Abayomi Olonisakin, da kuma hafsan sojojin kasa na kasar, Yusuf Tukur Buratai su gabatar da sojojin da ake zargi suna da hannu a sakin Hamisu Wadume a gaban kotun.

Kotu karkashin jagorancin alkali Binta Nyako ta dage zama sauraron zuwa ranar Litinin 30 ga watan Maris 2020.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More