Kotu ta dage zaman sake yin duba a kan hukuncin zaben Imo da Zamfara

Kotun kolin Najeriya ta dage zaman sauraron sake yin duba a kan kararrakin da aka shigar gabanta wadanda ke kalubalantar hukuncin da  kotun kolin ta zartar  na korar tsohon gwamnan jahar Imo Emeka Ihedioha, daga kan kujerarsa da kuma soke nasarar da jam’iyyar APC ta samu a zabukan 2019 da aka gudanar na matakai daban-daban a ta jahar Zamfara.

Lauyan Ihedioha da PDP mai suna Kanu Agabi mai mukamin SAN ne ya nemi a dage karar domin bai wa bangarorin damar kammala shirye-shirye nasu.

Lauyan Uzodinma da APC Damian Dodo SAN, bai kalubalanci bukatar da  PDP ba.

Alkalin alkalan  na kasar Najeriya  Mai shari’a Tanko Muhammad, ne ya  jagoranci alkalai bakwai a sauraron karar ta Ihedioha da mambobin APC na Zamfara suka yi na  kalubalantar hukuncin kotun.

Kotun kolin  ta dage karararrakin ne zuwa ranar 2 ga watan Maris na 2020.

 

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More