Kotu ta haramtawa Onnoghen rike mukami tsawon shekaru 10 a Najeriya

Kotun da’ar ma’aikata ta yanke wa Mai shari’a Walter Onnoghen hukunci bayan karar da gwamnatin Najeriya ta shigar na zarginsa da kin bayyana kadarorinsa.

Kotun ta tsige shi daga mukaminsa kuma ta saka masa takunkumin hana shi rike mukamin gwamnati na shekaru goma tare da kwace kudaden da ke asusun ajiyarsa na banki, inda gwamnatin ta mayar da su mallakarta.

A kwanakin baya ne gwamnatin kasar ta bukaci Alkalin Alkalan kasar, wanda aka dakatar mai sharia Walter Onnoghen da ya dakatar da aikinsa kan zargin da ya shafi kin bayyana kadarorin da ya mallaka.

Daga bisani kuma ta gurfanar da shi gaban kotun da’ar ma’aikata.

Sai dai Onnoghen din ya daukaka kara, inda ya kalubalanci dakatarwar da aka yi masa a kotu. Sai dai kotun ta yi watsi da kararsa daga baya.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More