Kotu Ta Mallakawa Gwamnati Najeriya Kudin Matar Jonathan naira miliyan 9.2 da dala 8.4

Babbar Kotun Tarayya da ke birnin jahar Legas ta bayar da umurnin karbe  wasu makuden kudade wajen  uwargidar tsohon shugaban kasar Najeriya  Patience Jonathan domin mallakawa gwamnatin kasar

Kudaden da kotun ta karba  daga hannun  Patience Jonathan sun hada da Naira miliyan 9.2 da kuma Dala miliyan 8.4 da ake ajiyar su a bankunan Diamond da Fidelity, Eco, Stanbic, Skye, Zenith da kuma  First Bank.

An zartar da hukuncin karbar makuden kudaden ne bayan da  lauyan Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Kasar Najeriya, Rotimi Oyedapo ya gabatar da kudurin karbe kudaden baki daya a gaban Mai Shari’a Mojisola Olatoregun a shekarar 2018.

Babu wasu gamsassun hujjojin da za su hana ayyana kudaden a matsayin wandanda aka same su ba ta haramtattun hanyoyi ba.

Patience Jonbathan ta bayyana wa kotun cewa, ta samu kudaden ne daga gudummawar da wasu mutanen kirki ‘yan Najeriya suka bai wa gidauniyarta a lokacin da mijinta ke kan kujerar mataimakin gwamnan Bayelsa da lokacin da ya zama gwamnan jahar har zuwa lokacin da ya zama shugaban kasar Najeriya.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More