Kotu ta rushe sabbin sarakunan Kano da gwamna Ganduji ya kirkira

Menene ra’ayin ku game da hukuncin kotun?

Babbar kotun jihar ta ce ta yanke wannan hukunci ne saboda an shigar da kudurin bukatar kirkirar masarautun ba bisa ka’ida ba.

Ga dukkan alamu dai wannan hukunci na babbar kotun na nufin yanzu sarki daya ne a Kano ba biyar ba kamar yadda aka kirkira a ‘yan watannin da suka gabata.
Barista Ibrahim Mukhtar shi ne lauyan bangaren gwamnatin jahar, kuma ya shaida wa BBC cewa kotu ta yanke hukuncin ne ba tare da tsayawa ta yi bincike yadda ya kamata ba.
Wani lauya mai suna Ibrahim Salisu ne ya fara gabatar da bukatar kirkirar sabbin masarautun a Kano da sunan kamfaninsa. Kwanaki kadan da yin hakan ne kuma majalisar ta yi wani zama don tabbatar da dokar.

Amma a ranar Alhamis da take yanke hukuncin, kotun ta ce ba a san inda kamfanin nasa yake ba, kuma ya kasa bai wa kotun gamsasshiyar hujja game da koken nasa.
Ta kuma ce Ibrahim ba shi da hurumin da zai shigar da batun majalisa har a yanke hukunci cikin kwana uku.
Kotun ta ce majalisar ta take dokar kundin tsarin mulki na 1999 da ke bai wa majalisun jiha damar yin dokoki. A don haka ne ta ce ta soke dokar gaba daya.

Tsohon shugaban marasa rinjaye na majalisar jihar, Nasiru Muhammad Gwarzo ne ya shigar da kara kotun yana kalubalantar dokar majalisar, saboda a cewarsa ba a sanar da shi cewa an koma zaman majalisa ba don yin kudurin, kuma kundin tsarin mulki ya bukaci sai an sanar da shi.
A don haka, kotun ta ce cikin dalilan yanke hukuncin nata har da rashin bin ka’idar sanar da dawowar majalisa.
Maliki Kuliya shi ne lauyan Nasiru Gwarzo, ya ce kotu ta yi abin da ya dace, kuma akwai alamar adalci. “Dama mun jima muna fadar haka.”

Duk da faruwar al’amarin gwamnatin jahar Kano tana da damar daukaka kara daga yanzu zuwa kwana 90.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More