Kotu ta soke takarar Adeleke na Jahar Osun

Babbar Kotun tarayyar  Abuja dake Bwari ta soke takarar Ademola Adeleke na jam’iyyar PDP kan  zaben gwamnan Jahar Osun da aka gudanar a watan  Satumba, 2018.

Mai Shari’a Othman Musa ne ya yanke hukunci bayan ya bayyana cewa sanata mai wakiltar jahar Osun ta yamma Adeleke ya kasa gamsar da kotun cewa ya kammala makarantar gaba da faramare wato Sakandare, kamar yadda ka’idar shiga takarar gwamna da Kundin dokokin kasar ta Najeriya Sashe na 177 ta gindaya na.

Adegboga Oyetola na APC ya  samu nasarar lashe zaben da aka gunadar a cikin Satumba inda Ademola Adeleke yasha kaye.

Sai dai daga bisani  Adeleke ya kai kara kotu yana cewa shi ya samu nasarar lashe zaben ba Adegboga Oyetola na APC ba.

Hakan yasa ranar Juma’a  22 Ga Maris, Babbar Kotun Tarayya ta bai wa Adeleke nasara, tare da cewa zaben da aka maimaita a wata rumfa ranar 27 ga Satumba, wanda ya bawa dan takarar APC nasara, haramtacce ne, domin bai kamata a sake maimaita zaben ba.

Yayin da  kotun ta umarci INEC ta bai wa Adeleke takardar shaidar samu nasara a zaben da ya gudana.

Sai   dan  takarar APC, Adegboga Oyetola ya hanzarta garzayawa kotun daukaka kara tare da kalubalantar hukunci da kotu ta yanke na  soke nasarar tashi da ta yi. Sai ga shi kuma kotu ta yanke hukunci a baya-bayan nan inda ta ce takardun Adeleke na kammala Sakandare bana gaske bane, wato jabu ne.

Sanata Adeleke ya shaida wa kotu cewa ya kammala Muslim High School, Ede dake Jahar Osun, sai dai kuma  babu sunansa a cikin jerin daliban da suka kammala makarantar a cikin 1980.

Duk da cewa ya hada wasu shaidu da suka kammala makarantar a lokaci daya, kotu ta ce an gano cewa sunansa ya fito ne a cikin sunayen wadanda suka rubuta jarabawar Turanci ne kawai.

Adeleke dai ya ce shi ma zai daukaka kara kar zuwa kotun koli ta kasa.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More