Kotu ta soke zaben yan majalisu na APC a Sokoto ta bawa PDP

Kotun Daukaka Kara a Sakkwato ta kori Majalisar Dattawa Abubakar Shehu Tambuwal da dan majalisar wakilai Hon. Aliyu A. A Shehu na jam’iyyar APC.

Kotun ta tabbatar da Ibrahim Abdullahi Danbaba a matsayin dan majalisar ma wakiltar Sakkwato ta Kudu da kuma Dakta Shehu Balarabe Kakale dukkanin su an jam’iyyar PDP.

Mai Shari’a Fredrick Oho ya bayyana cewar kotun ta yi fatali da hukuncin kotun karar zabe, ta kuma gamsu da dukkanin hujjojin masu kara. Alkalin ya ce Sanata Abubakar Shehu Tambuwal da Aliyu A.A Shehu na jam’iyyar APC ba su cancanci zama yan takara ba, hakkan yasa kotun ta umurci hukumar zabe mai zaman kanta wato INEC da ta karbe takardar shaidar lashe zabe da ta ba su ta kuma baiwa Ibrahim Danbaba da kakale takardar shaida lashe zabe tare da rantsar da su a Majalisar Tarayya.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More