Kotun  daukaka kara taki amincewa da shaidu Abba gida-gida

Kotun daukaka karar zaben gwamna dake a jahar Kano, ta dakatar da bukatar dan takarar gwamnan jahar na  karkashin jam’iyyar PDP wato Abba Kabiru Yusuf.

Kotun  ta gudanar da sauye-sauye a jerin sunayen shaidun da zasu tsaya Abba  a gabanta.

Abba Kabir ya shigar da bukatarsa a gaban kotun na neman samun damar sauya kurakuran dake  cikin jerin sunayen shaidun da za su tsaya masa a gaban kotun, inda ya nema Karin sunayen shaidu guda  takwas kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

Babban lauya mai wakilcin dan takarar na jam’iyyar PDP Adegboyega Awomolo, ya ce babu wani nufi na sauya sunayen shaidun da suka gabatar face bukatar kara sunayen wasu shaidun takwas da a halin yanzu kotun ta ki amincewa.

Yayin shimfida dalilai da take zartar da hukunci, Mai shari’a Halima S. Muhammad, ta ce kotun ta yi watsi da wannan bukata ta jam’iyyar PDP ne duba da girma da kuma bijirowarta a kurarren lokaci, wanda hakan ya sabawa ka’idojin ta shari’a.

 

 

 

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More