Kotun daukaka kara tayi umarnin sake zaben dan majalisar APC na Kogi

Kotun daukaka kara da ke zama a Abuja ta soke zaben  dan majalisar wakilai mai wakiltan mazabar Ajaokuta Mohammed Lawal na jahar Kogi na karkashin jam’iyyar APC.

Lawal, ya samu  nasara a karar da aka shigar kotun kararrakin  zaben na  jahar da farko, sai dai Dan takarar jam’iyyar PDP Aloysius Okino, ya daukaka kara, inda ta kotun ta zatar da hukunci wajen umurtar  hukumar zabe mai zaman kanta  wato INEC da ta sake gudanar da sabon zabe a rumfunar zabe 21 da ke mazabar.

Sai dai bayan yanke hukuncin ne, yan kwanaki kadan kotun koli ta tsige Mohammed Lawal na APC mai wakiltan Lokoja/Kogi a majalisar wakilai sannan ta kaddamar da Barista Shaba Isah Ibrahim na PDP a matsayin wanda ya lashe zabe.

 

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More