Kotun koli ta tabbatar da Abba Kabir

Kotun Kolin Najeriya ta tabbatar da Injiniya Abba Kabir Yusuf a matsayin halattaccen dan takarar gwamnan jahar Kano karkashin jam’iyyar PDP a zaben da ya gabata.

Alkalan kotun sun tabbatar da hukuncin Kotun Daukaka Kara ta Kaduna wacce ta yi watsi da bukatar Ibrahim Al’amin (Little) na cewa PDP ba ta yi zaben fitar da gwani ba.

Kotun ta ce (Little) wanda ya yi nasara a kotun farko a Kano, ba shi da hurumin shigar da kara kan zaben da bai shiga ba. Abba Yusuf, wanda aka fi sani da “Abba gida-gida”, ya sha kaye a hannun Gwamna Abdullahi Umar Ganduje a zaben da aka gudanar, duk da cewa shi ne kan gaba a zaben farko wanda aga bisani a sanar da rashin kammaluwar zaben.

Masu sa ido na gida da waje sun kalubalanci  yadda aka gudanar da zaben wajen cewa magudi aka tafka.

Jam’iyyar APC tare da hukumar zabe mai zaman kanta  sun musantar zargin nasu.

Jam’iyyar PDP  tare da dan takarar ta sun shigar da kara a kotun saurarar kararrakin zabe, inda suke kalubalantar nasarar  Gwamna Ganduje.

 

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More