Krepin Diatta ya koka kan yadda wasu ke ci masa fursa kan muninsa

Krepin Diatta ya ce yayi  matukar bakin ciki da yaga wasu yan uwansa, yan Afrika suna tsokanar sa  ta tare da ganin muninsa.

Ina matukar kokarin ganin na kare  martabar yankina na Afrika amma dariya, zagi, cin zarafi da aibata launin fata ta shi na samu a matsayin sakamako inji shi.

Yace a tunanin  sa gayon baya ya kamata ya samu a wurin su,ba zagi da kuma aibata hallitar da Allah yayi masa ba.

Inda ya kara da cewa yana godiya Allah mahallancin sa da ya bashi lafiya ba tare da ya hallarci shi muskini ba, da kuma masoyan sa daka son sa.

Diatta  ya bayyana  sau 28 shekarar 2018 zuwa 2019 inda ya samu nasarar jefa kwallo biyu a raga tara da shirin samu wasu nasarar guda biya a gaba, ba a yi tsammani ba karawar sa da Tanzania ya kasance ya samu nasarar jefa kwallo daya a ragar su, wanda ya zame masa kwalla ta farko taya samu nasarar wanda aka buga  ta kasa da kasa da Senegal.

A karshe Krepin Diatta  yace dariya mutane ba abun da zata sauya man a  rayuwata, sannan kuma kuma abun da sani  dukkan mu dai yan Afrika ne.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More