Kungiyar Dattawan Arewa Sun bukaci a kyale yan kabilar Igbo su balle daga Najeriya idan sun fi son hakan

Dattawan na arewa sun kuma lura cewa har sai Igbo sun yanke shawara ko suna son ballewa ko kuma su ci gaba da kasancewa a cikin Najeriya,

Kungiyar Dattawan Arewa (NEF) ta ce ya kamata a bar Igbo su balle daga Najeriya idan hakane yankin kudu maso gabas suke so.

Da yake zantawa da manema labarai bayan wata ganawar sirri da aka yi a Abuja a ranar Litinin, Hakeem Baba-Ahmed, mai magana da yawun kungiyar Dattawan Arewa, ya ce hargitsin da Ibo ke yi na ballewa ya yadu, yana mai cewa kamar shugabannin sun nuna goyon bayansu ga shirin nasu na ballewar.

Baba-Ahmed ya ba da shawarar cewa yin fito-na- fito da masu karajin neman ballawar zai kara tabarbarewar rashin tsaro a kasar.

“Wannan al’ummar ta sha fama da mummunan yaki domin kiyaye kasar. Arewa ta ba da gudun mawarta a wannan yakin, kamar yadda ta yi ta hanyoyi da yawa a tsawon tarihin kasar. A karkashin halin da muke ciki yanzu, babu wani dan Najeriya da zai yi maraba da wani yakin don kasar ta ci gaba da zama a dunkule, ”inji shi.

“Taron ya kai ga matsaya mai wuya kan cewa idan goyon baya ga ballewa a tsakanin Ibo ya yadu kamar yadda ake yadawa, kuma ga alama shugabannin Ibo suna goyon baya, to ya kamata a shawarci kasar da kada ta kalubalanci hakan.

“Ba zai zama mafi kyawu ba ga ‘yan kabilar Ibo ko ‘yan Najeriya su bar kasar da dukkanmu muka yi wahala mu ka gina ta kuma kasar da dukkanin mu ke da alhakin gyarawa ba, amma ba zai taimaka wa kasar da tuni ta yi fama da gazawa a durkushe ba sake yin wani yaƙi don ci gaban zaman Ibo a Najeriya. ”

Kungiyar ta yi gargadin cewa dole ne a daina kai hare-hare da kashe-kashen ‘yan arewa, ma’aikatan gwamnatin tarayya, da lalata dukiyar kasa, ta kara da cewa dole ne a kamo wadanda ke da hannu a gurfanar da su.

Dattawan na arewa sun kuma lura cewa har sai Igbo sun yanke shawara ko suna son ballewa ko kuma su ci gaba da kasancewa a cikin Najeriya, doka ta yi aiki a kanta, tunda gwamnatocin tarayya da na jihohi suna da aikin tabbatar da doka da kuma kare ‘yan kasa.

Sun kuma goyi bayan kiraye-kirayen da ake yi wa ‘yan arewa da ke fuskantar musgunawa da tashin hankali, da su yi tunanin sake komawa arewa.

Duk da haka, sun ba da shawarar cewa ya kamata a karrama dukkan Ibo da sauran kabilun da ke zaune a arewacin kasar kamar yadda aka saba da kariyar su.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More