Kungiyar KCCI a bukaci zaman lafiya a Jahar Kano

Wata kungiya ta al’umman Jahar Kano, masu son zaman lafiya da ci gaban Jahar sun  shelanta cewa, dattawan Jahar ba za su sanya ido su bari son ran wani ko wasu gungun mutane ya jefa Jahar a cikin rikici ba.

Shugaban kungiyar, Bashir Tofa, tare da wasu jigajigan kungiyar sun  bayyana hakan ne a  lokacin da suke magana da manema labarai a kan yanda lamurran siyasa jahar Kano, ke daukar hankali musamman ma da aka samu rashin kamaluwar zabe a zaben da aka gudanar na 9 ga watan Maris, wanda hukumar zabe mai zaman kanta wato INEC ta bayyana hakan.

Yace, dattawan zu suyi dukkan abun da ya dace dan ganin a samun zaman lafiya tare da kin bin ra’ayin duk a ya son zaman lafiyar Jahar.

Tofa wanda ya taba  takarar shugaban kasar Najewriya karkashin jam’iyyar NRC, ya kara da cewa kungiyar ta su ta KCCI ta damu matuka da yanda sabani ke ta haihuwa a Jahar ta Kano.

A karshe yayi kira ga shugabannin siyasa da su guji furta zantukan da za su haddasa rikici, inda ya nemi jami’an tsaro da su kasance a ankare tun daga yanzun har zuwa lokacin da za a shelanta wanda ya lashe sakamakon zaben da za a sake a Jahar.

 

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More