Kungiyar Kwadago ta yi watsi da Naira dubu 27 mafi karancin albashin

Kungiyar Kwadago ta Kasa NLC ta yi watsi da Naira 27,000 a matsayin sabon mafi karancin albashi kamar yadda majalisar jahohin Najeriya ta amince da shi a taron da ta gudanar jiya Talata 22 ga watan Junairu 2019

Sakataren kungiyar, Dakta Peter Ozo-Eson, ya bayyana wa manema labarai haka a Abuja.

Ya kara da cewa, majalisar ba ta da hurumin sake kayyade mafi karancin albashin bayan da hadaiddiyyar kwamiti a kan mafi karancin albashin ta tattauna ta kuma bayar da rahoton ta.

Abin takaici ne gwamnatin na jan kafa wajen mika dokar mafi karancin albashi ga majalisar kasa, ta kuma shigar da rage kudaden zuwa Naira 27,000 ta hanun wannan taron da aka yi jiya na majalisar jihohin tarayya, inji shi.

Dakta Ozo-Eson ya kuma kara da cewa, kungiyar kwadago ta shirya gudanar da taron gaggawa na majalisar zartarwar kungiyar ranar Jumma’a don ba gwamnatin tarayya wa’adin kwanakin da za su, mika dokar ga majalisar kasa domin amicewa.

Sakataren kungiyar ya kuma kara da cewa, gwamnatin tarayya na gayyatar gaggarumin yajin aiki ne kawai da wannan matakin da ta dauka a wannan karon.

Ya kamata kowa ya fahinci matakin da za mu dauka bayan taron kwamitin zartarwa da za mu gudanar ranar jumm’a,’’ 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More