Kungiyoyin kwadago taki amincewa da 24 mafi karancin albashi

Kungiyoyin kwadago a Najeriya sun nuna rashin gamsuwarsu game da matakin  da gwamnatin kasa ta dauka wajen   gabatar da naira dubu 24 a matsayin mafi karancin albashin ma’aiktan kasa ta Najeriya

Ministan kwadago na kasar Chris Ngige, ya shaida wa manema labarai cewa bayan tattaunawa da gwamnonin jihohi ne gwamnatin tarayya ta amince da Naira dubu 24 a matsayin mafi karancin albashin ma’aikata.

An  tattaunawa  hakan ne tsakanin gwamnatin tarayyar kasar da kuma kungiyoyin kwadago, wadanda suka yi wani yajin aikin gargadi mako biyu da suka wuce.

Yayin da sakataren tsare-tsare  Nasir Kabir yace matakin da Gwamnatin ta dauka gama da na batun mafi karancin albashin ya zama kamar was an yara.

Hakan yasa kungiyar kwadago kasa NLC a Najeriya tace baza ta  amince da adadin wannan kudin, domin bah aka zuka shirya a farko ba.

Sakataren tsare-tsaren ya ce, idan har gwammnati ta gaza biya musu bukata a kan albashin, to akwai matakai da za su dauka, da suka hadar da sake tafiya yajin aiki, sannan kuma duk inda suka san akwai ma’aikatansu a ko ina a fadin kasa, to za su janye su daga wajen.

 

You might also like More from author

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Comment moderation is enabled. Your comment may take some time to appear.