Kwallon kafa

• Real Madrid na hakon daukar dan wasan gaban Manchester City Raheem Sterling mai shekaru 24, a cewar Mirror.

• Kocin Real Madrid Zinedine Zidane ya gargadi mai tsaron ragar kungiyar dan kasar Belgium Thibaut Courtois mai shekaru 26 kan rashin kokarin da yake yi, in ji jaridar Sun.

• Ita ko La Gazzetta Dillo cewa ta yi; Uefa ka iya dakatar da dan wasan gaban Juventus Cristiano Ronaldo mai shekaru 34 saboda alamar zagi da ya yiwa magoya bayan Atletico Madrid a wasan da suka buga na zagaye na 16 na gasar Zakarun Turai.

• Da yiwuwar dan wasan bayan kasar Faransa Samuel Umtiti mai shekaru 25 ya koma Manchester United a karshen kakar wasa ta bana idan ya bar Barcelona, a cewar Calceomercato.

• Jaridar Sun ko cewa ta yi; dan wasan gaban Chelsea da kasar Faransa Olivier Giroud mai shekaru 32 ya ce babu damar cigaba da zama a Chelsea muddin ba a bashi cikakkiyar damar doka wasa ba.

• Tuni kocin Manchester United mai rikon kwarya Ole Gunnar Solskjaer ya yanke shawara kan yan wasan da za su bar Old Trafford a karshen kakar wasa, yayin da ake da tabbacin dan wasan bayan kasar Ecuador Antonio Valenci mai shekaru 33 zai bar kungiyar, a cewar shafin Manchester Evening News.

• Sannan kuma an yi imani da cewa Arsenal na sahun gaba cikin kungiyoyin da ke zawarci Valencian, bayan mahaifinsa ya yi furucin cewa tabbas zai bar Manchester United, in ji Metro.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More