Kwallon kafa : Neymar, Coutinho, Munir El Haddadi, Willian

• Kafar Goal ta ruwaito cewa Barcelona za ta siyar da Coutinho don samun kudin da za ta dawo da tsohon dan wasanta Neymar.

• Neymar din da jaridar El Mundo ta yi ikrarin cewa ya kira Barcelona har sau biyar a yunkurinsa na ganin ya dawo kungiyar. Jaridar ta ce maihaifin Neymar ya tattauna da shugaban Barcelona Josep Maria Bartomeu, ya kuma ce dan nasa ya yi dana sanin komawa PSG.

• Goal din dai ta ruwaito cewa Munir El Haddadi na shirin barin Barcelona ya koma Sevilla.

• Jaridar Marca ta ruwaito cewa dan wasan ya ki amince ya sabunta kwantiragensa da Barcelona, kuma ya amince da komawa Sevilla.

• Haka nan kuma jaridar Marca ta ruwaito cewa ita ma Atletico Madrid ta bi sahun Sevilla wajen zawarcin El Haddadi wanda idan Barcelona sayar da shi a wannan watan ba dan wasan zai bar kungiyar a kyauta lokacin da kwantiraginsa za ta kare a watan Yuni.

• Ita ko jaridar Telegraph cewa ta yi Chelsea ta ki amincewa da tayin da Barcelona ta yi mata na bata Malcom mai shekaru 21 don ta dauki dan wasan Willian mai shekaru 31.

• kafar Goal ta ruwaito cewa Bayern Munich na zawarcin dan wasan tsakiyar PSG Adrien Rabiot mai shekaru 23,wanda ake sa ran zai koma Barcelona a karshe kakar wasa

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More