Kwamitin SDG ta majalisar dattawa sun ki amincewa da wakilin Fashola

Jaridar Daily Trust  ta rawaito cewa kwamitin harkokin cigaba mai dorewa (SDG) a majalisar dattawa sun ki sauraron karamin Ministan ayyuka da gidaje wato Abubakar Aliyu.

Kwamitin na SDG ta bukaci Minista Babatunde Fashola ya zo gabansu dan yi  masu bayani,  amma sai ministan ya turo mataimakinsa inda majalisar dattawan taki gamsuwa  da hakan . Shugabar  kwamitin, Aisha Dahiru Binani, ta bukaci Tunde Fashola ya hallara a gabansu domin ya yi masu bayanin ksn abubuwan da  suka shige masu duhu.

Fashola ya tura Abubakar Aliyu ne domin ya kare kasafin ma’aikatar na shekara mai zuwa a gaban majalisar.

Yan kwamitin sun nuna cewa babu abin da za su karba daga hannun Abubakar Aliyu domin babban ministan su ke son gani a karan kansa kamar yadda su ka rika ganawa da shi a baya.

Cikin kwamitin an samu wanda ya koka, wajen cewa ministan ayyuka zai sabawa umarnin Buhari, ya yi tafiya ketare a daidai lokacin da ake aikin kasafin kudi.Inda Malam Abubakar Aliyu ya yi kokarin yi wa Sanatocin bayani cewa mai gidansa, Babatunde Fashola, ya bar Najeriya ne bayan ya samu iznin shugaba  Buhari,sai dai  ba su amince da haka ba.

Sanata Binini ta nuna fushinta ga yadda Ministan zai bar Najeriya bayan an sanar da shi game da zaman.

Hakkan yasa suka dauki wasu lokota na  jiran Raji Fashola har karfe, a karshe dai bai samu hallartar wajen ba.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More