Kwanaki kadan ya rage  NCC ta rufe kantin SIM miliyan 2

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta umarci Hukumar Sadarwa ta Kasa wato  (NCC) cewa, zuwa ranar 25 ga Satumba 2019 zata  rufe katin layukan sadarwa na layin waya wato  SIM card guda miliyan 2.224 wanda ba a yi wa rijista ba daga na’urar sadarwar kasar.

Ministan sadarwa Dakta Isa Ali Ibrahim Pantami, ne ya sanar da hakan a ofishinsa da ke babban birnin tarayyar  Abuja a lokacin da sabbin shugabannin hukumar NCC suka kai masa ziyara.

Ministan ya kara da cewa, bayan cikar wa’adin kwanakin da aka sanar wasu masu amfani da katin layukan sadarwan ba zasu samun damar yin amfani da shi ba.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More