
Kwankwanso ya rubutawa shugaba Buhari wasika kan mace-macen Kano
Tsohon gwamnan Jahar Kano dakta Rabiu Musa Kwankwanso ya rubutawa shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari wasika kan yawan mace-macen da ke faruwa a Kano. Kwankwaso ya bukaci gwamnatin tarayya ta gaggauta daukar mataki domin ceto rayukan al’umma jahar
A cikin wasikar da ya wallafa a shafinsa na Twitter, tsohon gwamnan ya ce ya rubuta wasikar ne saboda a cewarsa abin da ke faruwa a Kano abin tsoro ne musamman yadda mutane ke mutuwa kusan a kullum tun bayan soma yaki da cutar Coronavirus da kuma sanya dokar hana fita da gwamnatin tayi a jahar Kano