Kwankwaso na so magoya bayansa su guji tayar da hankali

Tsohon gwamnan jihar Kano Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya yi kira ga magoya bayansa da su guji tayar da hankali bayan zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokokin tarayya.
Sanata Kwankwaso, wanda shi ne jagoran jam’iyyar PDP a jihar ta Kano, ya yi wannan kira ne bayan jam’iyyar APC ta yi nasara a kujerun majalisar dattawa da ta wakilai da ma shugaban kasa a jihar.
Ya ce za su dauki matakai na shari’a domin tabbatar da cewa rashin adalcin da aka yi musu bai dore ba.
A cewarsa, “Ina so na jawo hankalinmu cewa zaman lafiya shi ya fi komai muhimmanci; ka da wani ya dauki doka a hannunsa a kan wannan zabe.
“Muna fata mutane za su ci gaba da shirye-shirye na zaben gwamna da na ‘yan majalisar dokokin jiha.”

Ya kara da cewa sakamakon zaben shugaban kasa na ci gaba da nuna cewa babu tabbas kan wanda zai yi nasara har sai an kammala bayyana sakamakon.
Sanata Kwankwaso ya yi kira ga magoya bayansa musamman a jihar Kano da su sake daura damara domin kayar da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.
Gwamna Ganduje dai ya raba gari da Sanata Kwankwaso ne tun bayan da ya hau kan mulki a 2015.
Ana zargin Gwamna Ganduje da karbar cin hanci na daloli a wani faifan bidiyo da jaridar Daily Nigerian ta wallafa.
Sai dai gwamnan ya sha musanta zargin.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More