Kwararrun masu karanta lebe sun cimma matsaya game da batun Alvaro da Neymar

Masana karanta lebe sun tabbatar da cewa dan wasan bayan Marseille Alvaro Gonzalez ya zagi Neymar

Dan kasar Brazil din ya yi ikirarin cewa dan kasar Spain din ya furta masa kalaman nuna wariyar launin fata, wanda hakan ya haifar da fushin da ya ja aka kore shi lokacin da PSG da Marseille suka hadu a Ligue 1.

Yanzu, kafar watsa labaran Brazil Esporte Espectacular ta gudanar da bincike, inda ta kawo kwararru da dama a karatun lebe don tantance abin da aka fada.

Binciken ya tabbatar da cewa dan Spain din ya kira Neymar “biri”.

Sabbin hotunan da Mediapro ta wallafa a ranar Lahadi an yi amfani da su a Brazil don gano abin da aka faɗi kuma PSG za ta yi amfani da waɗannan hotunan don kare Neymar da kuma tabbatar da cewa Alvaro ya ci zarafinsa ta hanyar wariyar launin fata.

Bugu da kari, za su samar da wani masanin karatun lebe don tabbatar da abin da aka fada.

Alvaro na iya rasa buga wasanni 10 idan aka same shi da laifi.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More