Lafazin Buhari kan zabukan da basu kammalu a wasu jahohin ba

Fadar shugaban kasar Najeriya  ta gargadi magoya bayan jam’iyyar APC mai mulki kan cewa ba za ta saka baki cikin sakamakon zabukan ba da aka gudanar ba, musamman wayanda ba’a kammala ba.

Hukumar zabe ta Najeriya  mai zaman kanta wato INEC dai ta tsayar da ranar 23 ga watan Maris ne a matsayin ranar da za a kammala zabuka a jahohin kasar guda 5, wato Kano,Plateau, Adamawa, Sokoto, da kuma Benue.

A cikin wata takarda ta hannun mai bai wa shugaban kasar shawara kan yada labaru Garba Shehu, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce hukumar INEC ita ke da ruwa da tsaki kan dukkanin wani zabe da aka, kuma da  za a gudanar.

Inda Sanarwar tayi suka game da masu ganin laifin shugaban Buhari saboda rashin nuna ko-in-kula a kan zabukan da za a kammala a jahohin.

Sanarwar ta zargi wasu ‘yayan jam’iyyar APC mai mulkin kasar da kokarin ganin shugaban kasar ya yi amfani da karfinsa wajen ganin an murde sakamakon zaben.

Mai magana da yawun nasa, a cikin sanarwar ya ce kundin tsarin mulki bai ba wa shugaba Muhammadu Buhari ikon saka baki cikin harkar zaben kasar ba, saboda haka ba zai yi abinda ya karya dokar  kudin tsarin mulkin kasar ba.

Ya kuma kara da cewa hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya wato INEC, na cin gashin kanta ne, kuma za ta ci gaba da aikinta ba tare shugaba Buhari ya saka bakin sa ba.

Bayan gudanar da zaben gwamnoni a jahohi 29 na kasar, a ranar 9 ga watan Maris din shekara ta 2019, jam’iyyar APC ta lashe zabe a jahohi 13, yayin da PDP ke da jahohi 9.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More