Lai Muhammad ya kalubalanci masu yada labaran karya

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa yawaita samun labaran da basu da tushi da maganganun batanci, yana iya bada gudumnawa wajen kunna wutar rikici a kasar nan idan har ba a dauki wani matakin na gaggawa ba, domin akwai hadari sosai a tattare da labaran karya da maganganun batanci wanda ka iya kawo tangarda ga tsarin mulkin dimokaradiyya da kuma hadin kan kasa, tare da  barazana ga cigaban zaman Najeriya a matsayin kasa daya al’umma daya.

Ministan labarai Lai Muhammad,  ya bayyana haka a neyayin da yake tattaunawa da manema labarai a babban birnin tarayyar Abuja, ranar Talata 29 ga watan Oktoba 2019, inda yace gwamnati ba za ta lamunci watsa labaran karya ba, don haka za ta saka kafar wando daya da duk masu irin dabi’a.

Babu wata gwamnati da zata zuba  idanu wajen barin labaran karya su mamaye kafafen sadarwar, saboda hadarin dake tattare dashi, wanda  hakan na iya  kunna rikici tare da ruruwa bambamci tsakaninmu a kasar.

Dole ne mu cigaba da lalubo hanyoyin magance wanzuwar labaran karya da maganganun batanci a tsakaninmu har sai mun kawar dasu daga cikinmu.” Inji shi.

A karshe yayi kira ga yan jaridu da su baiwa gwamnati goyon baya bisa kokarin da take yi wajen kawo karshen labaran karya da maganganun batanci musamman a kafafen watsa labaran kasar.

 

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More