Lamarin Zamfara ya fi karfin shugaba Buhari

Fitattacen malamin addinin Islama wanda aka sani da, Shiekh Abdallah Usman Gadon Kaya, ya ce abubuwan da su ke faruwa na kashe-kashe da a ke yi a jahar Zamfara ya fi karfin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.

Ya bayyana hakan ne a wani faifan bidiyo da ya wallafa a shafinshi na Facebook, yayin da ya  bayyana abubuwa na rashin dadi da suke faruwa a Najeriya bisa son zuciya da neman duniya na wasu daga cikin manyan ‘yan siyasa da kuma jagororin Arewa su ke da shi. Lokacin fadar sunayen wayannan mutanen baiyi ba duba da cewa na san su.

 

Akwai arzikin ma’adanai a Zamfara,  shine dalilan da ya sa a ka fara tada fitina a jahar Zamfara.Domin samun damar diban  ma’adanai na jahar,hakan yasa ya kafa misali da dajin Sambisa inda yace  saboda danyen mai da ya ke daji ya sa a ka fara fitintinu dan a kautar da hankalin gwamnati inda ta nan ne za’a samu damar  sace albarkatun kasar.

Ya kara da cewa , Shugaba Muhammadu Buhari ya na da masaniya a kan duk abubuwan da su ke faruwa a Zamfara, sai dai ba shi da karfin da zai iya yin abu saboda al’amarin ya fi karfinshi, sai da taimakon wadansu.

Idan ya tura sojoji ko ‘yan sanda, su ma su na da masu ba su umarni. Cikin manyan sojoji su ma su na da son su sami kudi.

Al’umma da dama na ganin cewa shugaba Buhari ne yake da damar da zai yi duk mai yiwuwa wajen daƙile waɗanann abubuwa marasa daɗi kama daga garkuwa da mutane, harbin kan mai uwa da wabi da saurarn al’amura da suka gagare alummar kasar ta Najeriya.

 

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More