Lauyoyi 65 Kauran Bauchi ya dauka dan kare nasarar lashe zaben da yayi

Zababben gwamnan Jahar Bauchi, Sanata Bala Muhammad ya ce, ya riga ya hango zamun nasarar karar da Gwamna mai ci, Barista Muhammad Abubakar da jam’iyyar APC ta shigar gaban kotun kararrakin zabe.

Sanata Bala ya bayyana hakan ne a yayin da yake ganawa da manema labarai a ranar Asabar13 ga watan Afrilu.

Zababben gwamnan ya dauki lauyoyi har guda 65, yayin da 5 daga cikinsu manyan lauyoyi ne wato (SAN) don kare nasarar tashi a gaban kotun kararrakin zaben.

Har yanzu ba a kawo mana bukatar kotun ba, don haka har yanzu bamu san mai ake tuhumar mu ba, in suka kawo mana takardar kotun za mu san mai ake ciki. Inji Kauran Bauchi.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More