Likitoci sun shiga yajin aiki a Najeriya

Daya daga cikin manyan kungiyoyin kwadago na likitoci a Najeriya ta ce ta soma yajin aiki ranar Litinin saboda rashin isasshen albashi da kuma kayan kariya musamman ga likitocin da ke yaki da cutar Covid19.

Gamayyar Kungiyoyin Likitoci masu neman kwarewa ta ce za ta daina aiki daga Litinin ciki har da na gaggawa da kula da masu cutar ta Coronavirus.

BBC ta rawaito cewa,Shugaban kungiyar, Aliyu Sokomba, ya ce gwamnati ta gaza cika sharudan da aka gindaya mata, wadanda suka hada da kira da ta kara albashi ga likitocin da ke cikin kasadar kamuwa da cutar Coronavirus.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More