Likitocin Najeriya sun janye daga yajin aiki da suka tafi

Likitocin Najeriya sun janye daga yajin aikin da suka dauki tsawon sati daya suna yi don nuna rashin jin dadinsu bisa rashin isasshen albashi da kayan kariya na yaki da cutar coronavirus.

Kungiyar likitoci ta National Association of Resident Doctors (Nard), wacce ke wakiltar kashi 40 na likitocin kasar, ta ce ta janye daga yajin aikin ne bayan gwamnati ta amince ta biya mata bukatunta, a cewar sanar da kungiyar ta fitar a yau Litinin 22 ga watan Yuni 2020.

Sai dai ta ce yajin aikin bai shafi yada take gudanar da aikin yaki da cutar ta coronavirus ba.

Ta kara da cewa tuni gwamnati ta soma biyan bukatunta, wadanda suka hada da dawo a likitocin Asibitin Koyara na Jami’ar Jos da kuma ta umarci babban likitan asibitin ya biya albashinsu da aka rike.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More