Ma Shiryin Fina-Finan Hausa Ya Siya Wa Jaruma Ummeeduniyarnan Mota

Daya daga cikin jarumar  fina-finan hausa,  wato Ummi El’Abdul wacce a ka fi sani da ummeeduniyarnan  itama ta bayyana a shafin ta Instagram, cewa Shaharanren ma shiryin fina-finan kannywood da shriye-shiryen na gidajen talabijin wanda aka sani  da Alhaji Sani Sule Katsina  ya siya mata mota mai kira Honda Accord 2006 wacce take kaiwa kimanin dubu dari takwas (800,000)

Jaruma Ummi El’Abdul ya bayyana wa OaKTVHausa cewa tana alfahari da Sani Sule Katsana domin kamar uba yake a gurinta,  sannan  har cikin gidan su yake shiga a Jahar Katsina duba da cewa yan gari daya ne, kuma ya san har iyayen ta.

Sanna ta kara dacewa duk wanda ya santa a  fadin masana’antar kannywood to ya santa ne da  Sani Sule Katsina kuma bata da abun da zaka ce da Sani  sai dai tace Allah ya kara masa  arziki, domin kusancin ta da Sani  Sule yafi karfin wasa, dan haka duk wanda zai ce wani abu akan siya mata  motar da yayi wanda ba alkairi ba, to ya rage nashi.

 

 

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More