
Ma’aikacin Facebook ya kamu da cutar Coronavirus
Kamfanin sada zumunta na Facebook ya ce wani ma’aikacinsa a ofishinsa na birnin Seattle a kasar Amurka ya kamu da cutar Coronavirus, kamar yadda wata mai magana da yawun kamfanin ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.
Kamfanin ya ce za a rufe ofishin har zuwa ranar 9 ga watan Maris kuma an bukaci ma’aikatansa da ke birnin da su yi aiki daga gida har zuwa karshen wata.