Ma’aikatan Lafiya 40 ne suka kamu da Coronavirus a Najeriya

Ministan Lafiya na Najeriya, Dr Osagie Ehanire ya bayyana cewa,ma’aikatan lafiya kusan 40 ne suka kamu da Coronavirus, yayin da suke aikin kula da masu cutar.

Dr Ehanire ya bayyana haka ne ranar Alhamis a wurin taron manema labarai da kwamitin yaki da Coronavirus ke gudanarwa  kullum kan irin matakan da ake dauka na yaki da cutar.

Saboda haka ya roki ma’aikatan lafiyar da su tabbatar sun  bawa kansu kariya sosai a lokacin da suke kula da masu cutar a koda yaushe.

Sannan kuma  ya yaba wa dukkan ma’aikatan lafiyar da ke kan gaba a yaki da annobar ta Covid19, tare da cewa  gwamnati za ta ci gaba da taikmaka ma’aikatan da duk kayan aikin da ake bukata na kare kai.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More