Ma’aikatan lafiya sun sake tafiya yajin aiki a Najeriya

Gamayyar kungiyar ma’aikatan lafiya a Najeriya ta Joint Health Workers Union (JOHESU) ta nemi ‘ya’yanta su fara yajin aiki a kasar baki daya tun daga yau Lahadi, 13 ga watan Satumba 2020.

Kungiyar ta dauki matakin ne bayan kwamitin gudanarwarta na kasa ya yi wata ganawa ranar Asabar, kamar yadda wata sanarwa da shugaban kungiyar Biobelemoye Joy Josiah ya sanya wa hannu a jiya Asabar ta bayyana.

JOHESU ta ce ta bai wa Gwamnatin Tarayya wa’adin kwana 15 domin a biya mata buƙatunta amma “babu abin da aka yi”.

Wannan yajin aikin na zuwa ne kwana uku bayan wata kungiyar likitocin ta National Association of Resident Doctors of Nigeria (NARD) ta janye nata yajin aikin da ta shafe kusan mako ɗaya tana yi.

Likitocin na neman Gwamnatin Tarayyar ta magance matsalar rashin kayan aiki a bangaren lafiya sannan ta biya bashin alawus-alawus da ma’aikatan yaki da annobar coronavirus ke bin ta.

Babu tabbacin irin girman tasirin da wannan yajin aiki zai yi ga yakin da Najeriya ke yi da annobar cutar Coronavirus,wadda har yanzu ake cigaban da samun sabin mutane da suke kamuwa ta cutar.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More