Mafi karanci albashi: Kungiyar kwadago ta koka bisa rashin aiwatarwa

Kungiyoyin kwadago sun yi kira ga ‘yan Najeriya da su gargadi gwamnatin tarayya kan aiwatar da albashi mafi karanci, inda suka kara da cewa dukkanin tattaunawar da su kayi da gwamnati kan albashi mafi karancin ya ci tura.
Akan hakan ne Kungiyoyin kwadagon take
Gargadi ga gwamnati cewa akwai yiwuwar za su shiga yajin aiki na gama gari muddin ba’a kaddamar da albashi mafi karancin ba.
 
Hadakan kungiyoyin ma’aikata da ke tattaunawa kan batun karin albashi sun bukaci ‘yan Najeriya su fadawa gwamnatin tarayya ta kaddamar da sabon albashi mafi karanci domin kare afkuwar yakin aiki. Tayi kirar ne a ranar Talata a birnin tarayya Abuja kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
 
Mukadashin shugaban kungiyar, Mista Achaver Simon da sakataren kungiyar Mista Alade Lawal sun ce yunkurin da kungiyoyin ma’aikatan su kayi na tursasa wa gwamnati ta kaddamar da albashi mafi karancin ya ci tura.
 
Sun ce kungiyoyin ma’aikatan sun bawa gwamnati isashen lokaci domin biyan bukatun ma’aikatan amma bisa ga dukkan alamu gwamnati ba za ta yi abinda ya dace ba har sai an gudanar da yajin aiki. Ya ce kungiyoyin ma’aikatan ba za su sake yi wa gwamnati gargadi ba kafin ma’aikata da ke jihohin Najeriya za su fara yajin aiki na rashin aiwatar da albashi mafi karanci da sauran gyare-gyare.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More