Mafi karancin albashi : Abun a yaba dubu 30 ta fara aiki – Ngige

Ministan kwadago na Najeriya, Dakta Chris Ngige, ya yi farin albishir da cewa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta fara biyan kananan ma’aikatan gwamnatin tarayya mafi karancin albashin na naira dubu talatin.

An fara kaddamar da wannan kudiri ne kadai a kan kananan ma’aikata daga matsayi na farko zuwa na shida, sannan yace manyan ma’aikata su kwantar da hakulan su gabanin sabon tsarin ya kawo gare su inji shi.

Ministan wanda ya bayyana hakan a birnin Enugu, ya yi watsi da ikirarin kungiyar kwadago ta Najeriya wadda ta ce gwamnatin tarayya ba ta da niyyar fara biyan mafi karancin albashin ma’aikata kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

Dakta Ngige ya ce kaddamar da wannan sabon tsari na fara biyan mafi karancin albashin dukkanin ma’aikatan babban kalubale ne da ba zai tabbata cikin lokaci kalilan ko cikin gaggawa ba face anbi daki-daki wajen shawo kan lamari. Yace sabon tsari ya fara tasiri ne a kan kananan ma’aikatan gwamnatin tarayya daga kan mataki na daya zuwa na shida. An sauya mafi karancin albashin kananan ma’aikatan daga dubu18 zuwa dubu 30.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More