Mafi karancin albashi : Har Yanzu ana bugawa Tsakanin Gwamnati Da Kungiyar Kwadago

Kwamitin da aka kafa domin ya duba yanda za a yi karin albashi a bisa sabon mafi karancin albashi na naira 30,000, ya sake kasa cimma wata matsaya bayan da wakilan gwamnatin tarayya da na kungiyoyin kwadago suka yi watsi da abin da aka yi shawarar karawa a wajen taron da suka gudanar bisa al’amarin.

Hakan kuwa duk da alkawarin da shugaban kasa ya yi na cewa gwamnatin tarayya da gaske take yi na fara yin aiki da sabon mafi karancin albashin, ta kuma nemi gwamnatocin Jahohi da suma su fara yin aiki da sabon tsarin albashin.

Taron kwamitin  da aka gudanar ya kare ne tare da yin kiki-kaka, bayan da wakilan gwamnatin tarayya a wajen taron suka dage da cewa, duk wani karin da aka yarda a yi tilas ne ya dace da naira biliyan 168 da aka samar a cikin kasafin kudin 2019, wanda za biya karin da aka yi a sabon mafi karancin albashin.

Wata majiya ta kusa da kwamitin wacce ba ta son a ambace ta a nan, ta yi zargin cewa, sa’ilin da kungiyoyin kwadagon suke bukatar a yi karin albashin da kashi 30 ga ma’aikatan da suke a matakin albashi na 14, ita gwamnatin tarayya tana bayar shawarar a yi masu karin kashi 9 da rabi ne a kan albashin na su. Majiyar ta kara da cewa, kungiyoyin kwadagon kuma suna bayar shawarar a yi karin albashi kashi 25 ne ga ma’aikatan da suke a matakin albashi na 15 zuwa 17, ita kuma gwamnatin tarayya a nata shawarar so take a yi masu karin albashin da kashi biyar kacal. Ya ce, “Abin da muke kokarin mu ga ya tabbata shi ne, gwamnati ta kara mafi karancin albashin ma’aikatan da suke a matakin albashi na 1 zuwa na shida.

 

Su kuma ma’aikatan da suke a matakin albashi na Bakwai zuwa na 14 a kara masu kashi 30 na albashin na su. muna kuma son a kara wa wadanda suke matakin albashi na 15 zuwa na 17 kashi 25 na albashin na su. hakan shi ne adalci, kuma hakan shi ne shawarar mu.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More