Mafi Karancin Albashi: Kungiyar kwadago zata dau mummunan mataki idan ba’a fara biyan dubu 30 kafin karshe shekara ba

Kungiyar kwadago ta Najeriya ta gargadi gwamnonin kasar da su fara biyan sabon mafi karancin albashi na naira 30,000 kafin 31 ga watan Disamba 2019.
Kungiyar ta yi wannan gargadi ne a wata sanarwar bayan taro da ta fitar na masu ruwa da tsakin kan sabon albashin.
Shugaban kungiyar Ayuba Wabba ya bukaci jahohin da ba su fara biyan sabon albashin ba su gaggauta kammala tattaunawa da sauye-sauyen da ake bukata kafin cikar wa’adin na 31 ga watan Disamban (Wato zuwa karshe shekarar nan da muke ciki)
BBC ta rawito cewa,Kunigyar kwadago ta NLC ta yi gargadin cewa rashin yin hakan kafin cikar wa’adin na iya haifar da mummunan sakamako da ba za ta iya bayar da tabbacin kawarwa da shi ba.

Mahalarta taron sun yanke shawarar yin aiki tare wajen tabbatar da aiwatar da biyan sabon mafi karancin albashin yadda ya kamata.
Sun tattauna kan sauye-sauyen da za a yi kan albashin ma’aikata bayan amincewar gwamnatin tarayya da naira 30,000 a matsayin mafi karancin albashi a kasar.
Taron ya samu halarcin shugabannin kungiyar na jahohi da takwarorinsu na kuniygar ma’aikata ta TUC da ministan ayyuka da wakilan gwamnatin tarayya da hukumar kwadago ta duniya.
Jahohin Adamawa, Jigawa, Kaduna, Kebbi da Legas sun kammala aiki a kan fara biyan sabon albashin, amma har yanzu Jigawa ba ta fara biya ba tukuna.
Wasu jihohi kuma sun kafa kwamitin tattaunawa da kungiyar kwadagon kan sauye-sauyen da suka shafi biyan sabon albashin.
Jahohin su ne Abia, Akwa Ibom, Bayelsa, Borno, Ebonyi Edo, Kano, Katsina, Neja,Ondo, Sokoto da Kuma Zamfara.
Wadanda ba su riga sun kafa irin wannan kwamiti ba su ne jahohin Bauchi,Yobe, Rivers, Benue,Gombe,Kwara Imo, Osun, Ekiti, Oyo, Anambra, Taraba,Cross River, Ogun, Enugu, Nasarawa, Plateau, Kogi, da kuma jahar Delta.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More